Article
Social Media · 7 min read
Za ka ga shafi yana da followers 100,000, 500,000 ko ma fiye da haka. Idan ka kalli adadin kawai, za ka ɗauka cewa shafin yana da matuƙar tasiri. Amma idan ka shiga cikin posts ɗinsa, sai ka ga wani hoto daban, engagement ya yi ƙasa, Comments kaɗan, Shares kaɗan, Mutane ba sa save. Idan business ne, followers ɗin ba sa zama customers. Idan organization ne, saƙonninsa ba sa samun irin response ɗin da adadin followers ɗinsa zai sa ka yi tsammani.
You can read the English version of this article here
A nan ne za ka fahimci cewa akwai bambanci tsakanin samun followers da kuma gina audience mai tasiri.
Followers masu yawa suna da amfani. Amma idan babu quality da relevance a cikinsu, wani lokaci adadin ya zama kamar decoration ne kawai a jikin profile.
Babbar Manufar Wallafa Content Ita Ce Ya Isa Ga Mutane Ya Kuma Yi Tasiri
Me ya sa muke wallafa content a social media?
A sauƙaƙe, muna son mutane su gani kuma su yi wani response.
Wani content muna son mutane su karanta.
Wani muna son su yi like ko comment.
Wani muna son su share domin ya isa ga wasu.
Wani muna son su save saboda yana da amfani.
Idan business ne, wataƙila muna son content ɗin ya taimaka wajen kawo enquiry ko sales.
Saboda haka, idan muka wallafa content kuma mutane suka gani, suka yi engagement mai kyau, suka share, suka save ko suka ɗauki action ɗin da muke so, wannan yana nuna mana cewa content ɗin yana yin tasiri.
Amma samun babban follower count ba ya tabbatar da cewa waɗannan abubuwa za su faru.
Rashin Fahimtar Target Audience
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suke jawo wannan matsala shi ne rashin kula da target audience.
Ba kowane follower ne ya dace da kowane shafi ba.
Idan kana gina shafi, ya kamata ka fahimci irin mutanen da kake son jawo wa shafin.
Su waye?
Me suke so?
Wace matsala ce suke son a warware musu?
Wane irin content ne yake da amfani a gare su?
Wane irin salo ne ya fi jan hankalinsu?
Idan shafi yana wallafa duk abin da ya ga dama ba tare da la'akari da audience ɗinsa ba, zai iya tara followers amma ya kasa gina alaƙa mai ƙarfi da su.
A social media, ba wai kawai ka samu mutane su danna Follow ba ne.
Ya kamata su samu dalilin da zai sa su ci gaba da kula da abin da kake wallafawa.
Wallafa Abin da Audience Ke Bukata
Wani kuskure kuma shi ne shafi ya mayar da hankali kawai kan abin da shi yake son wallafawa, ba tare da fahimtar abin da audience ke son gani ko abin da yake da amfani gare su ba.
Wannan ba yana nufin audience ce za ta tsara maka duk abin da za ka wallafa ba.
Manufarka da niche ɗinka suna da muhimmanci. Amma a cikin wannan niche ɗin, dole ka fahimci interests, behaviours da needs na mutanen da kake magana da su.
A nan ne content strategy take da muhimmanci.
Kada ka yi post saboda kana da abin wallafawa kawai. Ka wallafa abin da yake da alaƙa da audience ɗinka kuma zai ba su dalilin kulawa da kai.
Inactive Followers
Ba duk follower da kake gani a follower count yake active ba.
Akwai mutanen da suka daina amfani da account ɗinsu, akwai waɗanda suka follow shafin shekaru da suka wuce amma interest ɗinsu ya canja, akwai waɗanda suka yi follow saboda wani post guda ɗaya da ya yi viral amma ba su da wata alaƙa ta gaske da sauran content ɗin shafin.
Saboda haka, shafi zai iya kasancewa da followers masu yawa amma active audience ɗinsa ya yi ƙasa sosai.
Wannan shi ne dalilin da ya sa follower count kaɗai ba zai ba ka cikakken hoton ƙarfin shafi ba.
Canja Niche Na Iya Barin Ka da Followers Waɗanda Ba Su Dace da Kai Ba
Ka ɗauka shafi ya gina followers 300,000 yana wallafa wani nau'in content.
Daga baya sai ya canja akalar shafin gaba ɗaya zuwa wani niche daban, adadin followers ɗin yana nan, amma shin mutanen da suka follow saboda tsohon content ɗin suna da interest a sabon content ɗin? Ba lallai ba.
A nan za ka iya samun babban followers count amma relevance na audience ya yi ƙasa.
Mutane suna nan a matsayin followers, amma ba su ne mutanen da sabon direction ɗin shafin yake buƙata ba.
Rashin Consistency
Audience tana buƙatar ta san abin da za ta rika tsammani daga gare ka.
Idan yau kana active, gobe ka ɓace, ka dawo bayan wata ɗaya, ka sake yin posting na wasu kwanaki sannan ka sake ɓacewa. Wannan yana iya raunana alaƙar shafi da audience ɗinsa.
Consistency ba wai kawai yin posting kullum ba ce. Yana nufin samun tsarin aiki mai dorewa, kiyaye quality da kuma ci gaba da ba audience ɗinka dalilin bibiyar shafin.
Account ko Page Health Ma Yana da Muhimmanci
Wani lokacin matsalar ba content ko followers kaɗai ba ce. Lafiyar account ko page ɗin kanta na iya zama wani factor.
Idan shafi yana da matsaloli da platform policies, restrictions ko wasu account-health issues, hakan na iya shafar yadda content ɗinsa yake samun distribution.
Saboda haka idan shafi mai manyan followers yana samun unusually low performance, bai kamata a tsaya kallon content kaɗai ba.
A duba audience.
A duba consistency.
A duba content direction.
A kuma duba lafiyar account ko page ɗin.
Na San Shafuka Masu Dubban Ɗaruruwan Followers Amma Tasirinsu Ya Yi Ƙasa
Wannan ba magana ce da nake yi a theory kawai ba, akwai shafuka da na sani masu followers 500,000, wasu ma fiye da haka, amma idan ka kalli tasirin content ɗinsu, ba ya dacewa da girman followers count ɗinsu.
A gefe guda kuma, za ka iya samun shafi mai followers da ba su kai nasu ba, amma idan ya wallafa content sai ka ga comments, shares, saves da sauran meaningful engagement.
Idan business ne, audience ɗin tana iya zama customers.
Idan organization ne, mutane suna sauraron saƙonsa kuma suna responding.
Wanne ne ya fi amfani?
Shafi mai followers 500,000 da audience ɗinsa ba ta kula da abin da yake wallafawa?
Ko shafi mai followers 50,000 da kaso mai kyau daga cikinsu suke genuinely interested da abin da yake yi?
Adadi yana da muhimmanci.
Amma quality da relevance suna da muhimmanci fiye da adadi shi kaɗai.
Followers Masu Yawa Suna da Amfani, Amma Kada Su Zama Babbar Manufa
Ba ina cewa followers count ba shi da amfani ba. Yana da amfani. Girman audience na iya ƙara reach, credibility da damar da content zai isa ga mutane masu yawa. Amma matsalar tana farawa ne idan tara followers ya zama babban objective, maimakon gina audience mai amfani.
Idan duk abin da kake yi shi ne neman hanyar da mutane za su danna Follow, kana iya samun babban adadi ba tare da gina tasirin da kake nema ba.
A ganina, mutane da organizations ya kamata su rage fafutukar tara followers kawai.
Su ƙara mayar da hankali wajen gina audience.
Audience da suka san dalilin da ya sa take bibiyarka.
Audience da suke da interest a niche ɗinka.
Audience da suke kula da content ɗinka.
Audience da suke interacting da kai.
Audience da idan ka wallafa abu mai amfani suke karantawa, commenting, sharing ko saving.
Kuma idan business kake yi, audience da za ta iya zama customer.
Ka Gina Audience, Followers Za Su Biyo Baya
Wannan shi ne babban abin da nake ganin ya kamata mu fahimta.
Kada ka gina social media presence ɗinka domin follower count kawai. Ka gina audience mai amfani da tasiri.
Ka fahimci target audience ɗinka.
Ka san abin da suke buƙata.
Ka yi content da yake da amfani gare su.
Ka kasance consistent.
Ka kiyaye direction na shafinka.
Ka kula da lafiyar account ɗinka.
Ka gina trust da relationship.
Idan ka yi waɗannan abubuwan yadda ya kamata, ba kawai za ka samu audience mai quality ba.
Followers ɗin da mutane suke fafutukar nema su ma za su zo a matsayin sakamakon gina audience ɗin yadda ya kamata.
Saboda a ƙarshe, follower count yana nuna mana yawan mutanen da suka taɓa danna Follow.
Amma tasiri yana nuna mana yawan mutanen da har yanzu suke kula da abin da kake faɗa.
Continue exploring
More practical ideas and professional conversations.
Join the conversation
Share a thoughtful response to this Insight.