← All insights
Insight journal
Digital Media·Hausa·4 Sept 2026

Ƙarancin Hausawa a Fannonin Fasahar Sadarwa Abin Takaici Ne: Sai Yaushe Za Mu Farka?

A wasu manyan tarurrukan da na jagoranci ayyukan Livestreaming, na lura da ƙarancin Hausawa a muhimman fannoni na fasaha. Me ya sa muke baya idan an zo wurin ƙwarewa ta zahiri, kuma me ya kamata mu yi domin kawo kanmu gaba?

Written byAwaisu Al'arabee Fagge6 min read
Kayan AIkin Media Na Wani Babban Taro

Article

Digital Media · 6 min read

Akwai wata tambaya da take yawan zuwa min a rai a duk lokacin da na halarci manyan tarurruka da ake gudanar da manyan ayyukan fasaha:

Me ya sa muke ganin ƙarancin Hausawa idan an zo wurin ayyuka na zunzurutun ƙwarewar fasaha?

Wannan abu yana matuƙar ba ni takaici.

Domin idan kana kallon yadda muke cika social media da activities iri-iri, za ka iya tunanin cewa muna da tarin ƙwararru a fannoni daban-daban. Amma sau da yawa idan na shiga manyan tarurruka inda ake buƙatar ƙwararru domin gudanar da ayyukan fasaha na gaske, sai na nemi mutanenmu na rasa.

Zan bayar da misalai biyu daga abubuwan da na gani da idona.

Abin da Na Gani a MULAN National Annual Conference 2026

Na halarci National Annual Conference na MULAN na 2026, wanda aka gudanar a Kano.

An gayyato ƙwararrun media da fasaha a fannoni daban-daban domin gudanar da ayyukan taron.

- Akwai professional photographers.

- Akwai ƙwararrun masu video coverage.

- Akwai masu sarrafawa da haska abubuwan taron a majigi.

- Akwai sound engineers da suke kula da sautin taron.

- Akwai livestreamers.

- Da sauran ƙwararru a fannoni da dama da ban ambata ba.


Ni kaina na kasance a wurin ne saboda an gayyace ni domin na jagoranci Livestreaming, tare da wasu ayyuka.

Amma abin da ya ba ni mamaki shi ne, banda ni da wanda na je tare da shi domin ya taimaka min wajen aikin, Salis Muhammad Nasir Taraba, ban ga wani Bahaushe cikin manyan technical personnel ɗin da suke gudanar da ayyukan ba.

Akwai wasu matasa Hausawa guda biyu tare da sound engineers, amma su ma ba su ne suke gudanar da babban aikin sound ɗin ba. Abin da na gani sun fi mayar da hankali ne wajen kula da kayan aiki.

Kuma fa wannan taron ya gudana ne a birnin Kano.

Wannan ya sa na ƙara tambayar kaina:

Ina ƙwararrunmu suke?

Na Sake Ganin Haka a JIBWIS/Rabida International Conference 2026

Na sake halartar JIBWIS/Rabidah International Conference na 2026 wanda aka yi a Abuja, inda a nan ma na kasance wanda ya jagoranci Livestreaming.

A wannan taron ma an gayyato ƙwararru da yawa.

- Professional photographers.

- Masu video coverage.

- Graphic designers.

- Visual designers.

- Cameramen.

- Masu sarrafawa da haska abubuwan taron a majigi.

- Sound engineers.

- Livestreamers.

- Da sauran ƙwararru a fannoni daban-daban.


Idan aka tara yawan technical personnel da suke aiki a wurin, sun haura mutum 30.

Amma abin takaici, banda team ɗinmu mutum biyar da muka kula da Livestreaming, ban ga wani Bahaushe ko ɗaya cikin sauran ƙwararrun da suke gudanar da waɗannan ayyuka ba.

Wannan shi ne abin da yake damuna.

Hayaniya Da Surutu A Social Media Na Iya Sakawa Mu Ɗauka Cewa Muna Gaba

Idan mutum ya hau social media ya kalli irin hayaniyar da muke yi, zai iya tsammanin muna da tarin ƙwarewa.

- Content ko'ina.

- Creators ko'ina.

- DJs ko'ina.

- Mutane suna ɗaukar titles iri-iri na sana'o'i da ƙwarewa.


Amma idan aka je wurin da ake buƙatar zunzurutun fasahar aiki, sai ka nemi mutanenmu ka rasa.

A social media kuma, wani babban kaso na energy ɗinmu yana ƙarewa ne a soki burutsu, cin mutuncin juna, gulma, rigingimu da wasu content marasa wani amfani na zahiri ga cigabanmu.

Ba wai babu Hausawa masu yin abubuwa masu kyau ba.

Akwai su. kuma akwai ƙwararrun da suke abin a yaba. Amma tambayar ita ce:

Shin yawansu da matakin ƙwarewarsu sun kai inda ya kamata mu kasance a yau?

Mu Ma Da Ake Ganin Mun Iya Wasu Abubuwan, Idan Muka Shiga Cikin Wasu Ƙwararrun Ɓacewa Muke Yi

Ba na faɗin wannan domin alfahari ko domin in nuna cewa ni na kai wani mataki na musamman. A'a.

Ko mu da al'ummar da muke rayuwa a cikinsu suke ganin mun iya wasu abubuwa, wallahi wani lokaci idan muka shiga cikin wasu ƙwararrun sai mu ga kamar mun ɓace. Saboda sau da yawa suna yi mana nisa. A nan ne mutum yake ƙara fahimtar cewa ƙwarewa ba ta da iyaka. Duk abin da kake ganin ka iya, akwai wanda ya fi ka. Kuma maimakon hakan ya sa mu karaya, sai ya sa mu ƙara dagewa:

- Mu ƙara koyo.

- Mu ƙara bincike.

- Mu ƙara practice.

- Mu ƙara bibiyar yadda waɗanda suka fi mu suke gudanar da ayyukansu.

Yawan Masu Kayan Aiki Ba Yana Nufin Yawan Ƙwararru Ba

Wani lokaci idan ka kalli al'ummarmu, za ka ɗauka muna da DJs masu yawa.

Amma da yawa daga cikinsu abin da suka fi sani shi ne zuwa gidan biki, kunna waƙoƙi a yi rawa, shi ke nan.

Alhali audio da sound profession duniya ce mai faɗi.

Haka nan za ka ga muna da adadi mai yawa na content creators.

Kuma gaskiya akwai masu yin abubuwa yadda ya kamata a cikinsu.

Amma kuma akwai tarin content da bai wuce shiririta, hayaniya da neman attention kawai ba.

Wannan shi ne bambancin da ya kamata mu fara fahimta:

Yawan mutanen da suke amfani da technology ba yana nufin yawan mutanen da suka ƙware a technology ba.

Kuma mallakar kayan aiki ba ita ce ƙwarewa ba.

Mu Rage Korafin Cewa An Bar Mu a Baya

Sau da yawa muna korafin cewa an bar Arewa a baya.

- An bar Hausawa a baya.

- Wasu sun rigaye mu.

- Ba a ba mu dama.


Wataƙila akwai wuraren da wasu daga cikin waɗannan korafe-korafen suke da tushe. Amma akwai tambayar da ya kamata mu ma mu yi wa kanmu:

Mu kuma me muka yi domin dawo da kanmu gaba?

Ba za mu iya zama muna korafi kawai ba, muna jiran wani ya zo ya ɗauke mu ya kai mu inda muke son zuwa.

- Dole mu tashi tsaye.

- Dole mu dage da koyo.

- Dole mu yi nazari da bincike.

- Dole mu yi practice.

- Dole mu nemi ilimi daga waɗanda suka fi mu.

- Dole mu daina gamsuwa da ƙaramin abin da muka iya.

Kuma Idan Mun Iya, Mu Fito da Kanmu

Akwai kuma wani ɓangare mai muhimmanci.

Ba wai kawai mu koyi sana'a mu iya ba, sannan mu zauna babu wanda ya san muna yi.

Idan ka ƙware, ka fito da aikinka.

- Ka gina portfolio.

- Ka nuna projects ɗin da ka yi.

- Ka raba ilimin da ka samu.

- Ka sa wanda yake neman ƙwararren mutum a fanninka ya iya gano ka.

Domin akwai yiwuwar muna da wasu ƙwararrun Hausawa da suke iya aiki sosai, amma babu wanda ya san da zamansu saboda ba sa fito da ayyukansu. Saboda haka muna buƙatar abubuwa biyu:

Mu iya. Kuma duniya ta san mun iya.

Sai Yaushe Za Mu Farka?

Wannan ita ce tambayar da nake son mu yi wa kanmu.

Sai yaushe za mu rage hayaniya mu ƙara ƙwarewa?

Sai yaushe za mu rage content marar amfani mu ƙara amfani da damar da technology ta kawo mana wajen koyon sana'o'in da za su gina rayuwarmu?

Sai yaushe za mu daina korafin cewa an bar mu a baya, mu tashi mu yi abin da zai dawo da mu gaba?

Mu ma mutane ne.

Mu ma za mu iya.

Babu wani ilimi ko wata fasaha da aka halitta domin wasu mutane ne kawai ba domin mu ba.

Abin da ake buƙata shi ne mu dage da koyo, nazari, bincike da practice.

Mu nemi ƙwarewa ta gaske.

Sannan idan mun iya, mu fito da kanmu.

Duniya ta san muna yi. Kuma ta san mun iya.

Reader discussion

Join the conversation

Share a thoughtful response to this Insight.

Comments are reviewed before they are published.

Continue exploring

More practical ideas and professional conversations.

Browse all insights Discuss this topic